A wani sako da ta wallafa a shafin X, hukumar kwallon kafa ta Amurka ta ce “Babu shakka, babu wuri a cikin wasa na irin wannan halayya ta nuna kiyayya da wariya.”
Sanarwar ta kara da cewa “Wadannan ayyukan ba kawai ba za’a amince da su ba ne, amma kuma sun saba wa kimar mutuntawa da hada kai da muka dauka a matsayin hukuma.”
Timothy Weah, wanda bakar fata ne, yana daya daga cikin ‘yan wasan da aka ci zarafin su. An bai wa dan wasan gaba na Amurka jan kati kai tsaye a minti na 18 da fara wasa, saboda hannu da yasa ya bugi dan wasan Panama a bayan kan sa a lokacin da kwallo ta fita wajen filin wasa.
‘Dan wasan Amurka Folarin Balogun ya zura kwallo a minti na 22 da fara wasan bayan an bai wa Weah jan kati kafin dan wasan Panama Blackman ya farke a minti na 26.
Fajardo ya zura kwallon da ta bai wa Panama nasara da ci 2-1 a minti na 83.
Weah ya fitar da wata sanarwa ta kafafan sada zumunta, inda ya bayar da hakuri tare da neman gafarar wadanda ya bata wa rai.
Yanzu haka dai Amurka, wacce itace ke karbar bakuncin gasar cin kofin na Copa America, muddin tana son zuwa zagaye na gaba to dole ne tayi nasara a wasanta da Uruguay da zura kwallaye wanda ko da Panama ta yi nasara kan Bolivia za ta samu tsallake wa.