Palasdinawa zasu nemi 'yancin cin gashin kai

Workers use buckets to remove crude oil during a cleanup operation on the beach of Prao Bay on Samet Island, Thailand, July 30, 2013.

A yayinda yake fadin cewa Palasdinawa sun cancanci samun yancin cin gashin kai, shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya lashi takobin nemarwa Palasdinawa cikakkakiyar wakilci a Majalisar Dinkin Duniya a makon gobe idan Allah ya kaimu, duk da nuna rashin amincewar Isira’ila da Amirka.

Jiya juma’a Mr Abbas ya fadawa shugabanin Palasdinawa a birnin Ramallah na gabar yammacin kogin Jordan cewa, baiwa Palasdinawa cikakkiyar wakilci yancinsu ne ta halal, kuma zaije birnin New York da wannan bukata. Ya kuma ce tilas kasar Palasdinu ta samu kan iyakokinta na ainihi, na tun kafin Isira’ila ta mamaye yankunan Palasdinawa a alif dari tara da sittin da bakwai.

Ana sa ran cewa a ranar ashirin da uku ga wannan wata lokacinda Mr Abbas zaiyi jawabi a baban taron Majalisar Dinkin Duniya, zai gabatar da wannan bukata. Daga nan zai gabatar da bukatar baiwa kasar Palasdinu wakilci a Majalisar Dinkin Duniya ga kwamitin sulhu na Majalisar.

Jakadun Amirka dai suna ta safa da marwa tsakanin shugabanin Isira’ila dana Palasdinawa a wani yunkurin, fafardo da tattaunawar samun zaman lafiya tsakanin bangarorin domin kada Palasdinawa su gabatar da bukatar neman kasarsu ga Majalisar Dinkin Duniya. Isira’ida da Amirka dai basu goyon bayan wannan mataki. Shima Prime Ministan Isira’ila Benjamin Netanyahu a makon gobe zai yi jawabi gaban baban taron na Majalisar Dinkin Duniya.