Mayakan sa kai na Taliban saye farmaloli da aka cika da nakiyoyi suna dauke da rokoki da gurneti sun kai hari kan wasu muhimman wurare daban daban a Kabul babban birnin Afghanistan.Harin da suka kai a jiya talata ya halaka akalla mutane bakwai d a jikkata wasu goma sha tara.
Jami’an yanki sun ce an kashe akalla uku daga cikin maharani a hare hare d a suka auna kan helkwatar NATo, ofishin jakadancin Amurka da hukumar leken asirin Afghanistan, da wasu cibiyoyi masu yawa kusa da gundumar da manayan ofisoshin jakadancin kasashen duniya suke.
Har a can cikin daren jiya talata ana ci gaba da jin karar bindigogi da tashin bama-bomai, yayinda jami’an tsaron Afghanistan tareda da taimakon NATO suka sami galabar murkushe hare haren.
NATO da ofishin jakadancin Amurka duk suka ce babu daya daga cikin jami’ansu d a harin ya rutsa dasu.
A cikin sanarwa da ya bayar shugaban kasar Afghanistan Hameed Karzai, yayi la’anci harin ya kuma jinjinawa martani jami’an tsaron kasar suka dauka. Yace irin wadan nan hare hare ba zasu sa a tsaida matakan mikawa jami’an tsaro kasar harkar tsaro daga rundunar taron dangi na kas da kasa ba.
Kakakin NATO Janar Carsten Jacobson yace Taliban tana komawa ga ta’addanci ganin ta kasa samun nasara a faegb yaki.