Falasdinawa Zasu Ci Gaba Da Sallah a Masallacin Al-Aqsa

Tun bayan da kasar Isra'ila ta sanya tsauraran matakan tsaro a wurin Masallacin al-Aqsa, Musulmai a birnin Kudus suka fara nuna bacin ransu ta yin Sallah a wajen Masallacin.

Shugabannin addinin Islama a birnin Kudus sun ba Musulmai izinin sake shiga wurin babban masallaci mai daraja dake dadadden birnin don yin sallah, bayan da Isra’ila ta cire matakan tsaro na karshe da ta girke a wurin a farkon watan nan.

Falasdinawa sun fara murna kan tituna a zagayen masallacin a safiyar yau Alhamis bayan da leburorin dake aiki a wurin suka cire bangwayen karfe, da wasu shingaye, da na’urorin daukar bidiyo daga kofofin shiga wurin. Amma falasdinawan basu iya shiga wurin ibadar ba sai bayan wani kwamitinsu ya kammala duba cikin masallacin sosai.

Matakan tsaron da Isra’ila ta sanya a wannan wurin ibadar da suka hada da na’ura mai nuna karfe, an sanya su ne sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga larabawa suka kai ranar 14 ga watan Yulin nan wanda yayi sanadiyar mutuwar ‘yan sandan Isra’ila biyu.

Wannan matakin da Isra’ila ta dauka ya fusatar da musulman da ke birnin Kudus, wadanda suka dade suna zaton a hankali Isra’ila na neman ta mamaye wurin ibadar ne.