A wani mataki da ba a saba gani ba, Fira Ministan Pakistan Imran Khan a jiya Lahadi ya bada sanarwar cewa gwamnatinsa zata bada shaidar zama dan kasar ga dubun dubatan 'yan gudun hijira daga Afghanistan wadanda kasar ta basu muhalli na shekaru masu yawan gaske.
WASHINGTON D.C. —
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD da jami'an Pakistan, sun ce akwai 'yan Afghanistan milyan 2 da dubu dari bakwai, cikinsu har da milyan daya d a rabi, wadanda suka yi rijista a zaman 'yan gudun hijira.
Mutanen sun tsere ne daga rikicin kasar na shekara da shekaru kan batun addini, ko kabilanci, ko talauci da kuma dai fitintinu iri daban daban a Afghanistan.
Binciken da MDD tayi ya nuna cewa kimanin kashi 60 ckin dari na 'yan gudun hijirar Afghanistan walau an haife su a Pakistan, ko kuma an kai su kasar tun suna yara. PM Khan, yace al'ada ce a duk fadin duniya, idan aka haife ka a cikin kasa, to kai dan kasar ne.