Pakistan Tayi Godiya ga Kasa da Kasa

Pakistan Tayi Godiya ga Kasa da Kasa

Hukumomin kasar Pakistan sun aike da sakon godiya ga kasa da kasa karkashin inuwar MDD a dalilin daukan alkawarin tura Karin agajin da kudinsu ya haura Dola miliyan metan domin amsa kiran Karin taimakon d Pakistan ta nema domin tinkarar matwsalar ambaliyarruwar data afkawa al’ummar Pakistan.

MDD tayi zaman gaggawa ran Juma’a domin nazartar kiran da Pakistan tayi na neman agaji domin tinkarar matsalar ambaliyar ruwan da yanzu ke addabar al’ummar kasar Pakistan.

Jakadan Pakistan a MDD Abdullah Haroon shine ya mika godiyar kasarsa ga zauren taron MDD, yace wadanda ambaliyar ruwan tafi shafa a Pakistan sun fahimci cewa al’ummar kasa da kasa basu yi watsi dasu ba.

Babban Magakatardar MDD Ban Ki-moon, yayi kira ga kasa da kasa da suci gaba amsa kiran badaagajin gagagwa ga kasar Pakistan, domin kasar Pakistan na cikin wani halin kaka-ni-kayi a dalilin ambaliyar ruwa da ta shafe makonni tana afkawa kasar. Yace matsalolin da ambaliyar ruwan ke haifarwa za’a yi shekara dashekaru kafin kaiwa ga samun nasarar kauda su.