Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Farmaki Na Amurka Sun Gama Janyewa Daga Iraqi


Birged ta karshe ta sojojin kai farmaki na Amurka a Iraqi ta bar kasar a karkashin shirin shugaba Barack Obama na janye sojojin Amurka baki daya daga kasar

Birged ta karshe ta sojojin farmakin Amuirka da ta rage a Iraqi ta bar kasar, a yayin da aka doshi wa'adin da gwamnatin shugaba Barack Obama ta tsayar na ranar 31 ga watan nan na Agusta domin kawo karshen dukkan ayyukan kai farmaki a kasar Iraqi.

Kamfanonin dillancin labarai da gidajen telebijin na Amurka wadanda ke da wakilai a cikin rundunar sojojin dake janyewar sun tabbatar da janyewar Birged ta 4 ta sojojin tanka da ake kira "Stryker Brigade" da kuma runduna ta 2 ta sojojin kasa. Da asubahin yau alhamis aka bayar da rahoton cewa tankoki da motoci masu sulke na karshe na wannan birged sun tsallaka cikin Kuwaiti daga Iraqi.

Amma jami'an gwamnatin Amurka sun ce har yanzu ba a kawo karshen ayyukan farmakin a Iraq ba. Suka ce akwai wasu sojoji kalilan da suka rage na kai farmaki a cikin Iraqin. Su na daga cikin sojoji kimanin dubu 6 wadanda aka shirya za su bar Iraqi baki daya nan da karshen wannan wata.

A bayan sun janye, wasu sojojin na Amurka su dubu hamsin zasu rage a Iraqi domin horas da sojojin Iraqi tare da gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci.

Sojojin Amurka sun shafe shekaru fiye da bakwai su na gudanar da ayyukan kai farmaki a cikin kasar Iraqi karkashin wani shiri mai suna "Operation Iraqi Freedom" wanda tsohon shugaban Amurka, George W. Bush, ya kaddamar.

XS
SM
MD
LG