Anyi Girgizar Kasa Mai Karfin 7.2 A Pakistan

Taswirar kasar Pakistan.

Rahotannin dake fitowa daga kasar Pakistan na cewa wata girgizar kasa mai karfin bakwai da digo biyu a ma’aunin karfin girgizar kasa ta girgiza illahirin yankin kudu maso yammacin Pakistan a safiyar yau laraba

Rahotannin dake fitowa daga kasar Pakistan na cewa wata girgizar kasa mai karfin bakwai da digo biyu a ma’aunin karfin girgizar kasa ta girgiza illahirin yankin kudu maso yammacin Pakistan a safiyar yau laraba.

Mazauna biranen yankin musamman mafi girma na Karachi sun fi tagayyara.

Cibiyar ayyukan kimiyyar kasa ta Amurka tayi bayanin cewa girgizar kasar ta Pakistan ta bugi kasar ne da karfe daya da dakikai 23 na safiyar Pakistan, tsahon ramin da girgizar kasar ta haifar ya kai kilomita hamsin da biyar yamma da garin Dalbandin a lardin Baluchistan, lardin da yafi kowane yawan al’umma a yankin.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta (Pentagon) tace rundunar sojin Amurka a yankin kudu maso yammacin Afghanistan sun ji hucin afkuwar girgizar kasar saboda karfinta.Amma duk da haka, babu abinda zai shafi ayyukan sojin da Amurka ke aiwatarwa a Afghanistan.