Dan takarar mukamin mataimakin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar adawa ta APC, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi Allah wadai da yin amfani da sojojin haya da gwamnatin Najeriya ta dauko domin yaki da kungiyar Boko Haram.
Mr. Osinbajo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ta musamman da Muryar Amurka a lokacin wata ziyara da ya kawo kasar Amurka.
“Saboda yadda gwamnati ta yi wa harkokin sojin rikon sakainar kashi, yanzu mun samu kawunanmu a wani hali.”
Osinbajo dan takarar mataimakin shugaban kasar Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya kuma samu damar yin jawabi a gaban ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka da sauren kasashen Afrika a biranen Baltimore da Silver Spring, duk a jihar Maryland.
A makon da ya gabata, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gayawa muryar Amurka cewa akwai “masu taimakwa da harkokin fasaha” da ke aiki da sojojin Najeriya.
“Mun sayi kayan yaki, kuma idan aka sayo sababbin kayan fada, ana bukatar horas da masu amfani da su. Shi ne muka gayyato su domin samar da horo.”
Sai dai a ganin Farfesa Osinbajo yin hakan ba hujja ba ne.
“Babu wani dalili da zai sa sojojin Najeriya wadanda suka yi fice a duk fadin duniya, kamar yadda suka nuna a rigingimun kasashen waje da wanzar da zaman lafiya, a ce yau sai sojojin haya sun taimaka musu.” In ji Osinbajo.
Har ila yau Farfesan ya nuna damuwarsa kan irin halin da ‘yan gudun hijra ke ciki inda ya ce akwai bukatar a maida hankali kansu.
“Batun ‘yan gudun hijra na da matukar muhimmanci, saboda yankunansu da ke arewacin Najeriya na fama d matukar talauci, idan aka duba, za a ga talaucin arewa ya fi na kudu, saboda haka, dole ne mu duba wannan lamari.” Farfesan ya kara da cewa.
Your browser doesn’t support HTML5