Olympics: Tobi Amusan Ta Kai Zagayen Semi-finals

Tobi Amusan a wasannin Olympics na Paris

A ranar Alhamis za a yi zagayen na semi-finals a filin wasa na Stade de France da ke Paris.

‘Yar wasan tseren Najeriya Tobi Amusan ta kai zagayen semi-finals a tseren mita 100 na bangaren mata a gasar Olympics da ake yi a Paris.

Amusan wacce ta taba kafa tarihi na duniya a tsere ta lashe wasan ne a cikin 12:49 dakika.

Alaysha Johnson ta Amurka ce ta zo ta biyu cikin 12:61 dakika sai Janeek Brown ta kasar Jamaica ta zo ta uku cikin 12:84 dakika.

Ana sa ran Amusan za ta iya lashe kyautar zinare a gasar.

A wasannin Olympics da aka yi a Tokyo Japan, Amusan mai shekaru 27 ta gama a matsayi na hudu a tseren mita 100.

A ranar Alhamis za a yi zagayen na semi-finals a filin wasa na Stade de France da ke Paris.