Jean-Philippe Mateta ya zira kwallaye biyu a wasan da Faransa ta samu hayewa zuwa wasan karshe na gasar kwallon kafa ta maza a gasar Olympics ta Paris bayan da ta doke Masar da ci 3-1 bayan karin lokaci a jiya Litinin.
Faransa za ta fafata da Spain a wasan karshe a ranar Juma’a a Parc des Princes, wasan da zai tabbatar da kasar Turai ta farko da za ta samu lambar zinari bayan shekaru 32.
Faransa mai masaukin baki ta yunkuro a wasan da aka yi a Stade de Lyon ta doke kungiyar ‘yan wasan Masar wadda ta fara kai naushin farko ta kwallon da Mahmoud Saber ya zura a daidai minti 62 da wasa.
Sau uku Faransa ta ke shan karfen raga kafin daga bisani Mateta ya zura ta cikin raga a daidai minti 83 kana wasan ta shiga karin lokaci.
Kwallonsa ta biyu ta zo ne a daidai minti 99 bayan da alkali ya yi waje da dan wasan Masar Omar Fayed wanda ya samu katin gargadi sau biyu.
Yayin da wasan ya kai mintuna 108 ne kuma dan wasan Faransa Michael Oliseh ya zura kwallo ta uku.
Dandalin Mu Tattauna