OIC: Kungiyar Kasashen Musulmi Tayi Taron Neman Zaman Lafiya

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou mai masaukin baki

Yin la'akari da yadda matsalolin ta'adanci ke neman durkusar da ayyukan yawon bude ido koina a duniya ya sa kasashen musulmi suka yi taron duba hanyoyin dakile ta'adanci a kasashensu.

Taron na neman bullo da hanyar da za'a kare ayyukan bude ido fannin da yake samar masu kudaden shiga masu dimbin yawa kowace shekara musamman a kasashen da suka mallaki kayan tarihi da na al'adu.

Ministar ma'aikatar ayyukan yawon bude ido ta Nijar Madan Yahaya Ba'are Hajiya Hauwa tayi misali da harin da 'yan ta'ada suka kai kan wani otel a Mali wanda ya jawowa kasar babbar hasara da kuma rushe wurare masu dimbin tarihi na kasar da 'yan ta'ada suka yi duk da sunan addini.

Jihar Agades ta kasar Nijar ta dogara ne ga ayyukan yawon ido amma yau babu shi, yankin ya shiga cikin wani halin kuncin rayuwa saboda aika-aikar 'yan ta'ada kamar abun da kungiyar Boko Haram keyi yanzu a yankin Diffa.

Tace yanzu ko mutane na son zuwa wuraren ba sa yi. Tace ko taron da su keyi kasashe da dama suka ki halarta saboda tashin hankali a kasar wadda Boko Haram ke haddasawa musamman a yankin Diffa.

Taron ya samu jagorancin shugaban kasar Nijar din Muahamdou Issoufou wanda ya bude shi. Shugaban yace idan ana son a kubutar da duniya daga bala'in ta'adanci, to hakin yin hakan ya rataya ne akan mahukuntan kowace kasa.

Yace su shugabanni su dukufa da waye kan al'ummominsu da na sauran duniya su gane cewa kuskure ne mai muni 'yan ta'ada ke tafkawa. Yace a yi anfani da kafofin ilmantarwa da na fadakarwa domin cire akidar tsatsaurar ra'ayi daga zuciyar wadanda ke labewa bayan addini suna cutar jama'a.

Sakataren kungiyar musulmi ya jinjinawa shugabannin kasashen kan yadda suke fadi tashin fadakar da duniya manufofin musulunci dangane da zaman lafiya, abun dake nufin babu wata alaka ko kadan tsakanin addinin musulunci da ayyukan ta'adanci. Daga bisani ya cigaba da yiwa shugaban Nijar godiya cikin harshen Hausa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

OIC: Kungiyar Kasashen Musulmi Sun Yi Taro Akan Nemn Zaman Lafiya - 2' 34"