Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro Ya Tabbatar Da Tserewar Shugaban Kamfanin Binance Daga Najeriya

Binance

Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya tabbatar da tserewar manajan yankin Binance na Afirka, Nadeem Anjarwalla daga Najeriya.

WASHINGTON, D. C. - A wata sanarwa da Zakari Mijinyawa, shugaban yada labarai na ONSA ya fitar, ya ce "binciken farko ya nuna cewa Mr. Anjarwalla ya tsere daga Najeriya ta hanyar amfani da fasfo din da aka yi fasa-kwaurinsa".

Sanarwa ta kara dda cewar, an kama jami’an dake kula da tsaronsa kuma ana gudanar da cikakken bincike domin fayyace yadda aka yi ya tsere daga hannun hukuma

A ranar Litinin, wani rahoto da mujallar Premium Times ta wallafa, ya ce Shugaban Binance ya tsere daga Abuja inda aka tsare shi da abokin aikinsa, a ranar 22 ga watan Maris.

Anjarwalla dai ya tsere ne bayan da masu tsaronsa suka yi masa rakiya zuwa wani masallaci dake kusa domin sallah da addu'o'i na azumin watan Ramadan, inda daga bisani ya tsere.

Ana kyautata zaton ya bar daga Abuja ta hanyar bin wani jirgin sama mallakar wata kasa a Gabas ta Tsakiya saidai har yanzu ba a san yadda ya hau jirgin kasa da kasa ba duk da cewa fasfo dinsa na kasar Burtaniya ne.