Ofishin Jakadancin Faransa Ya Horas da 'Yan Jaridan Nijar Akan Zabe

Mahamadou Issoufou shugaban Nijar

A jamhuriyar Nijar an horas da 'yan jarida akan rawar da yakamata su taka a zaben kasar da zai gudana badi wanda ofishin jakadancin Faransa ya dauki nauyinsa.

Makasudin taron da ya samu halartar 'yan jarida sama da talatin daga gidajen radiyoyi da talibijan shi ne tunatar dasu irin rawar da yakamata su taka domin a kiyaye duk wani tashin hankali.

Duk abun da zai kawo rudani a lokacin da kasar ke gudanar da zabe kamata ya yi 'yan jarida su shawo kansa.

Mataimakin hukumar sadarwa ta kasar Nijar ya ce zasu yi zabe cikin kasar shekara mai zuwa kuma aikin jarid ba na tada wuta ba ne sai dai ya kasheta saboda a kwantar da hankulan jama'a.

Kamata ya yi su sa jama'a gaba tare da kiyaye dokokin aikin jarida domin kada su yi kuskure. Aikinsu ne su bada labarin da aka tabbatar.

'Yan jarida da suka halarci taron horon na tsawon kwanaki tara sun bayyana cewa sun samu daratsi sosai daga Mr Henry Vail wani kwararren dan jarida da aka gayyato daga kasar Faransa..

Wani Abduljalil Alhaji Sama dan jarida yace lokacin da aka dauka a baiwa 'yan jarida horo ya yi daidai. Sun samu horaswa na kwarai akan abubuwan da zasu yi lokacin zabe saboda su yi aikinsu bisa ka'ida.

Ga karin bayani daga rahoton Souly Mummuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Ofishin Jakadancin Faransa Ya Horas da 'Yan Jaridar Nijar Akan Zabe - 2' 05"