Ofishin Jakadancin Amurka A Nijar Ya Shirya Taro Ma Dalibai Masu Koyon Aikin Jarida

Taron Daliban Makarantar Aikin Jarida A Nijar

A Janhuriyar Nijar ofishin jakadancin Amurka ya shirya wani taro da nufin ganar da daliban makaranta aikin jarida, da dabarun tantance sahihancin labari ta yadda za su kauce wa fada wa tarkon masu baza labaran bogi a kafafen sada zumunta ta yanar gizo.

Taron Daliban Makarantar Aikin Jarida A Nijar

Matasa maza da mata kimanin 25 daga kungiyoyi masu zaman kansu, da daliban makarantar aikin jarida Iftic ne su ke samun wannan horo dake maida hankali akan hikimomin aikin jarida.

Jami’in kula da sha’anin ala’du a ofishin jakadancin Amurka John Dow ya ce aikin jarida na da matukar wuya a wannan lokaci mai sarkakiya. Ya ce kullum ake samun labarai kala kala amma ba dukansu ne ke amfanar jama’a ba.

Taron Daliban Makarantar Aikin Jarida A Nijar

Kungiyar ‘yan jarida mata APAC a Nijar ita ce ta zo da shawarar bayar da wannan horo ga daliban da ke karantar aikin jarida, matakin da shugabar wannan kungiya Ami Niandou ta ce rigakafi ne ga matasa..

Lura da yadda kafafen sada zumunta ke daukar hankalin matasa a yau, ya sa majalisar matasan Nijar CNJ shigar da nata mambobin domin su amfana da wannan horo inji ta bakin shugaban CNJ Alio Oumarou.

Taron Daliban Makarantar Aikin Jarida A Nijar

Makarantar Iftic ta yaba da wannan yinkuri na gwmanatin Amurka a bisa la’akari da yadda abin zai zama tasiri a kawunan daliban dake karantar aikin jarida.

Ga rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Ofishin Jakadancin Amurka A Nijar Ya Shirya Taro Ma Dalibai Masu Koyon Aikin Jarida