Obasanjo Ya Gana Da Fulani A Abekuta

Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gana da shugabannin Fulani da nufin jin matsalolinsu da yadda za a iya magance su.

A cikin bayanansu, shugabannin matasan sun bayyana cewa, muhimman abubuwan da suka dame su sun hada da yawan satar shannu, sacewa da garkuwa da mutane, da kuma fashi da makami da sauka janyo masu asara suka kuma kashe sana’a da suka gada kaka da kakanni da ya kai ga yanzu ‘ya’yansu basu da wata sana’a, ba ilimi, ba aikin gwamnati, ba gonakin kansu.

Shugabannin Fulanin sun ce yanzu haka an raba Fulani da kusan kashi talatin da biyar cikin dari na shannunsu, abinda ya zama cewa, wadannan matsaloli sun hana ‘ya’yan Fulani wata hanyar rayuwa idan ba ta aikata laifi ba.

Masu kula da lamura da Sashen Hausa ya yi hira da su, sun bayyana gamsuwa da wannan zaman da suka ce hanya ce ta samun masalaha. Yayinda suka yi kira ga kabilu da yankunan Najeriya su nemi hanyoyi sulhu da zaman lafiya.

Saurari cikakken rahoton Hassan Tambuwal daga Ibadan

Your browser doesn’t support HTML5

Obasanjo ya gana da Fulani-3:30"