Obama Yayi Magana Akan Jirgin Malaysia

Shugaban Amurka Barack Obama ya tattauna da Firayim Ministan Malaysia a zango na uku na ziyarar kasahen Asia hudu da ya ke yi - wanda wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 50 da wani Shugaban Amurka mai ci ya je Kudu maso gabashin Asia.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da su ka kira a yau dinnan Lahadi, Firayim Minista Rajib Razak ya bayyana godiyarsa ga Amurka saboda irin taimaka ma ta da ta yi wajen neman jirgin saman Malaysia da ya bace mai lamba 370.

Mr Obama ya yi alkawarin cigaba da bayar da dukkannin gudunmowar da ka yiwu wajen neman jirgin, wanda ya bace tun makwanni bakwai da su ka gabata.

Shugabannin biyu sun ce sun amince su daukaka muhimman huldudinsu zuwa kwakkwarar dangantaka, za su kuma ba da hadin kai kan yarjajjeniyar cinakayya ta Trans-Pacific da kuma ta hana yaduwar makaman nukiliya, wadanda a baya Malaysia ke adawa da su duka.