Obama ya bayyana hakan ne a jiya Talata a birnin Johannesburg, inda yaje domin halartar bikin cika shekaru 100 na shahararren mai yaki da tsarin wariyar launin fata Nelson Mandela da yana raye.
Zuwa wannan biki, shi ne babban taro irinsa na farko da Obama ya halarta, tun bayan da ya sauka daga karagar mulki a bara, bayan da ya kwashe shekaru takwas yana mulki.
“Kin amincewa da gaskiya, dabi’a ce da ta yi hannun babbar riga da tsarin dimokradiyya, dalilin kenan da ya sa ya zama dole mu jajirce wajen kare kafafen yada labarai masu zaman kansu, mu kuma himmatu wajen yaki da dabi’ar mayar da kafafen sada zumunta, dandalin nuna fushi da yada karerayi,” inji Obama
Tsohon shugaban na Amurka, ya kuma yi kira ga masu rajin kare dimokradiyya, da su yi koyi da Mandela, wanda ya jajirce tare da nuna fata na-gari, wajen ganin cewa makarantu suna koyar da matasa “darrusan da suka jibinci yin zurfin tunani a koda yaushe, ba wai kawai su rika yin biyayya, ba tare da sanin makomarsu ba.