Nuna Banbancin Kabila Ko Addini Ke Maida Hannun Agogo Baya A Najeriya: Kungiyar Fulani Kiristoci

PLATEAU: Shugabannin kungiyar Fulani Kirista

‘Ya’yan kungiyar Fulani mabiya Isa Almasihu sun jaddada batun hadin kan al’umma ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, wanda a cewarsu zai zama mafita ga matsalolin tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta.

PLATEAU, NIGERIA - A karshen taronsu na shekara-shekara da suka gudanar a Jos, fadar Jihar Filato, sun karfafa junansu kan muhimmancin sanin ababen dake kunshe a Littafi Mai Tsarki da kaucewa shiga ayyukan ashsha.

Shugaban kungiyar, Rabaran Aliyu Buba yace a wannan shekara ne kungiyar ta cika shekaru hamsin da kafuwa, don haka suka yi masu ruwa da tsaki don wanzadda zaman lafiya.

Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Istifanus Gyang ya yaba da gudunmowar kungiyar ne wajen samarda zaman lafiya.

Ku Duba Wannan Ma Jami'ar Usmanu Danfodiyo Ta Soma Shirin Fadada Hada Kan Fulanin Nahiyar Afirka Domin Magance Matsalar Tsaro

Wassu da suka halarci taron sun bayyana cewa zasu ci gaba da koyar da sakon zaman lafiya don samun ci gaba.

Fulani mabiya addinin kirista daga fadin Najeriya da kasashen Kamaru, Nijar, Burkina Faso da Mali ne suka halarci taron.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Fulani Kiristoci Sun Gudanar Da Taron Shekara-Shekara Na Kasashe A Jihar Filato