ABUJA, NIGERIA - NNPP wacce kimanin wata 3 ne kacal da bayyanar ta, ta tsayar da ‘yan takara a dukkan matakai na takara daga jihohi zuwa taraiya.
A wajen taron ganawa da ‘yan takarar jam’iyyar na gwamnoni a Abuja, NNPP ta ce dimokradiyya a Najeriya za ta yi armashi idan an samu adawa mai karfi fiye da yadda wasu ‘yan siyasa kan zabi sauya sheka zuwa jam’iyyar gwamnati bayan kammala zabe.
Dan kwamitin amintattun jam’iyyar Buba Galadima ya yi hasashen zuwa karshen shekarar nan jam’iyyar ta su ka iya gogayya ko ma ta wuce manyan jam’iyyu masu tasiri.
Sanata Halliru Jika wanda a kwanan nan ya fice daga APC zuwa NNPP don takarar gwamnan jihar Bauchi, ya ce nasara kan samu ne ta hanyar jajircewa da kusantar talakawa.
Haka shi ma dan takarar gwamna na jam’iyyar a Gombe Khamishu Ahmed Mailantarki ya ce ya kasance a adawa tun CPC ta shugaba Buhari zuwa NNPP amma har yanzu bai hakura da neman kawo sauyin da ya ke hankoro ba.
NNPP dai musamman a arewa ta hau kan doron siyasar mabiya tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ne.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5