NNPC Ta Warware Matsalar Tashin Farashin Makamashi Tsakanin ‘Yan Kasuwar Mai Da Kamfanonin Jiragen Sama

Hedikwatar NNPC

A daidai lokacin da kamfanonin jiragen saman Najeriya suka yi barazanan janye aikinsu na jigilan fasinjoji a fadin kasar sakamakon tsadan makamashin tafiyar da jiragensu nan da kwanaki biyu, kamfanin NNPC tare da hadin gwiwan mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar sun shiga tsakanin bangarorin .

ABUJA, NIGERIA . A ranar Litinin ne shugaban kamfanin jiragen saman jigilan fasinjoji na Airpeace, Allen Onyema, a madadin sauran kamfanonin jiragen saman kasuwa ya bayyana cewa nan da kwanaki kadan zasu janye aikinsu a fadin kasar a bisa dalilin gagarumin kari a farashin makamashin tafiyar da aikin jiragen saman nasu da ‘yan kasuwan mai suka yi ta yi musamman a baya-bayan nan, ya na mai cewa ‘yan kasuwan mai su fito fili su fadawa al’umma nawa su ke sayar da litarsu don a gano wa ke kwaruwa tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai jim kadan bayan da labarin matakin da kamfanonin jiragen saman ke shirin dauka ya kai ga wasu masu ruwa da tsaki a kasar, kamfanin man fetur na Najeriya tare da hadin gwiwar mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, sun shiga tsakani don samar da mafita mai dorewa in ji, shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari.

Mele Kolo Kyari

A sama da shekaru biyu da suka gabata aka fara fuskantar kari a farashin tikitin jiragen sama a Najeriya lamarin da a baya aka alakanta da durkushewar tattalin arziki sakamakon tasirin annobar coronavirus kafin tsadan mai na baya-bayan nan.

Tun ba yau ba ne fasinjoji masu zirga-zirga ta jiragen sama musamman don kasuwanci ke korafi kan tashin farashin tikiti.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulra’uf:

Your browser doesn’t support HTML5

NNPC Ta Warware Matsalar Tashin Farashin Makamashin Tsakanin ‘Yan Kasuwar Mai Da Kamfanonin Jiragen Sama