Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bukaci a saki shugabanta Joe Ajaero da jami’an tsaro suka kama yau Litinin nan take kuma ba tare da gindaya wani sharadi ba.
An kama Ajaero ne a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, akan hanyarsa ta zuwa Burtaniya domin amsa gayyatar kungiyar kwadagon kasar ta tuc.
Sanarwar da babban jami’in yada labaran NLC, Benson Upah ya fitar, tace kungiyar ta sanya kawayenta sauran kungiyoyin kwadago da rassanta na jihohi da kawayenta na kungiyoyin farar hula da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa cikin shirin ko ta kwana game da “wannan abin tashin hankalin dake faruwa.”
A cewar sanarwar, “an tsare Ajaero kuma har yanzu ba’a da tabbas game da inda yake ko kuma halin da lafiyarsa ke ciki, kasancewar duk wani yunkurin na tuntubarsa ya ci tura.”
Ku Duba Wannan Ma Hukumar DSS Ta Kama Shugaban Kungiyar Kwadago Joe Ajaero“Tsare shi cin zarafi ne karara kuma gaba daya babu wata dokar kasar nan da zata goyi bayan hakan. Iya tunanin hana dan kasa mai bin doka yin balaguro baya ga tauye masa ‘yancinsa na walwala sun isa yin fito na fito da tsarin dimokradiyya da ma hakkokinmu na al’umma kuma ma’aikata.”