Nikki Haley: Shugaba Donald Trump Bai Hanani Caccakar Rasha Ba

Jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya, Nikki Haley, ta fadi jiya Lahadi cewa Shugaba Donald Trump, bai hana ta caccakar Rasha ba, duk kuwa da cigaba da sukar kafafen labaran Amurka, saboda yadda su ke bayar da rahotanni game da binciken da Majalisar Tarayyar Amurka, ke yi kan ko wasu hadimansa sun hada kai da Rasha, don taimaka masa ya ci zabe ko a'a.

Ta ce "Shugaban kasa bai taba kira na ko sau daya ya ce, "Kar ki soki Rasha" ba, kuma bai taba kira na ya gaya mani irin abin da zan fada ba," inji Haley, wadda ta kara da cewa, "Ina caccakar Rasha, yadda ya kamata."

Haley, ta ce hade Crimea, a 2014 da Rasha, ta yi bai dace ba, haka ma cigaba da katsalandan da goyon bayan 'yan tawaye masu ra'ayin Rasha, wadanda ke gabashin Ukraine, kuma su ke yaki da sojojin Ukarine din.

"Muddun su ka aikata rashin daidai," in ji ta, "Babu abin da zai hana ni sukarsu. Kuma Shugaban kasa bai nuna rashin amincewa da hakan ba" wato nuna ma Rasha, "laifinta."

Da aka tambayeta ko Trump, ma na bukatar ya rika sukar Rasha, shi ma, sai Haley, ta ce, "A, i mana. To amma akwai abubuwa da dama gabansa, kuma bai hana ni caccakar Rasha ba."