Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe Maitaimakin Abu Bakr Al-Baghdadi A Wani Harin Jirgin Sama


 Abu Bakr al-Baghdadi
Abu Bakr al-Baghdadi

Gidan talabijin na kasar Iraqi yace An kashe Babban Mataimakin shugaban kungiyar Da’esh Abu Bakr Al-Baghdadi a wani harin jirgin sama da aka kai a yankin Al-anbar kusa da iyakar Syria.

Rahoton da ya fito a jiya Asabar yace Ayad Al-Jumaili tare da wasu kwamandojin kungiyar Da’esh an kashe su sakamakon harin jiragen sama na yaki da Dakarun Iraqi suka kai a nesa da Yammacin Iraqi. Rahoton bai bayyana lokacin da aka kai harin ba kuma bai bada wani ‘karin bayani akai ba.

Jami’an Amurka da ke jagorantar hadakar dakarun da ke yakar Da’esh basu tabbatar da mutuwar wannan Dan tsagera ba ya zuwa daren jiya Asabar.

A wani rubutaccen bayani da dakarun tsaron Iraqi suka bayar, rahoton ya bayyana Jumaili, wanda ake kira da Abu Yahya, a matsayin Ministan Yaki na Kungiyar Da’esh, rahoton yace Dakarun Sojin Saman sunyi shiri mai kyau kafin kai harin domin samun damar kai harin kan Helkwatar Da’esh wadanda ake kira a larabcin yankin da Al-Qaim.”

Jumaili mutumin da ada yayi aiki a matsayin jami’in tsaro a karkashin Saddam Hussein, Ya shiga cikin kungiyar ta ‘Yan Sunni bayan Mamayar da Amurka ta jagoranta a shekarar 2003, masu fashin baki sunce tun daga wannan lokacin ya zama yana karbar umarni ne kadai daga hannun Baghdadi.

Jami’an tsaron Amurka dana Iraqi sun hakikance Baghdadi ya maida mazauninsa kimanin kilomita 300 zuwa Arewa maso gabas, kuma a yanzu haka yana boye a cikin Sahara a wajen birnin Mosul.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG