Hukuncin da alkalin kotun yankin David Hale na Louisville, Kentucky ya yanke, ya bude kofar karar da wasu masu zanga zanga su uku suka kai cikin tsarin shari’a. An kai karar Mr. Trump da kuma wasu uku daga cikin magoya bayan sa.
Wadanda suka kai karar Henry Brousseau da Kashiya Nwanguma da kuma Molly Shah sun ce magoya bayan Trump sun ji masu ciwo a ralin da Trump yayi a watan Maris na shekarar 2016 a Louisville a yayin da Trump ya cigaba da cewa “Ku fita dasu.”
Alkalin ya rubuta ra’ayin sa kan cewa “Umarnin Trump na “Ku fita dasu” ya yi nuni da ayi amfani da karfi, Umarni ne kuma nuni ne na aiwatar da hakan.”
Sunayen mutane da ake karar ya haada da Matthew Heimbach mamba na kungiyar fifita fararen fata, da Alvin Bamberger mamba a kungiyar tsofaffin sojojin yakin Korea a Ohio, wanda ake karar na uku ba’a gano sunan saba tukunna.
Alkali Hale yace fitar da Nwanguma da ga wajen taron Anyi ganganci kuma Matar Bakar fata ta fuskanci tsanar Babbancin launi da kuma jinsi daga wajen mahalarta taron.
Hoton Faifan Vidoe na Heimbach da Bamberger a yayin da suke tura Nwanguma daga kan matakala yayin da Trump ke cewa ku fita dasu yayi yawo a kafafen Yada zumunta.
Facebook Forum