Jamhuriyar Nijer ta yi tur da yin anfani da iska mai guba a yakin basasan kasar Siriya.
WASHINGTON, DC —
Jamhuriyar Nijer ta shiga cikin jerin kasashen da suka yi alawadai da gwamnatin Siriya yayin da ta yi anfani da iska mai guba ta hallaka daruruwan jama'arta a cikin yakin basasa da yake gudana a kasar.
Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Nijer ya shaidawa kafofin labarai cewa kasarsa ta yi alawadai kuma ta yi bakin ciki da jin gwamnatin Siriya ta yi anfani da makamai masu guba kan mutane wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane mata da yara. Ya ce ba dai dai ba ne a kashe mutane da basu ci ba basu sha ba. Ya ce a dokar kasa da kasa an haramta yin anfani da irin wdannan makaman komi tsananin yaki. A hukumance suna kiran Majalisar Dinkin Duniya ta binciki lamarin ta kuma hukunta duk wadanda ke da hannu a lamarin.
Kokarin da wasu kasashen yammacin turai ke yi na shiga yakin, ministan ya ce wannan bai shafi kasarsa ba to amma domin abun zai taba rayuka da lafiyar dan adam dole su damu.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5