NIJER: Ministan Cikin Gida Ya Gargadi 'Yan Fafutuka Su Shiga Taitayin Su

Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar rushe kungiyar da ta shirya gangamin da ya rikide zuwa zanga zangar da ta haddasa barna a jiya lahdi a birnin yamai da nufin nuna adawa da tsarin kasafin kudin shekara 2018.

Da yake zantawa da wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka, Sule Mumuni Barma, ministan cikin gida Bazum Mohamed, ya bayyana cewa ‘yan siyasa na da hannu a wannan al’amari dalili kenan da ya gargadi ‘yan fafutuka su shiga taitayinsu.

Ministan ya bayyana cewa jam’iyya mai adawa ta dauki lokaci mai tsawo tana rabewa da guzuma tana harbin karsana, lamarin da ya faru a jiha lahadi ya tabbatar da haka.

Tarzomar ta jikkata Jami’an tsaro ashirin da uku, hudu daga cikin sun sami raunika masu tsanani, kuma yanzu haka suna asibi domin karbar magani.

Da yake ci gaba da bayani Bazum Mohamed, ya fadawa wakilin sahsen Hausa, cewar masu tarzomar sun lalata motocin ‘yan sanda guda Goma, da wasu guda hudu, da kuma sauran kayayyaki al’umma.

Daga karshe ya bayyana cewa ya rushe wata kungiya ta fararen hula wadda aka kitsa duk hayaniyar a karkashinta, ya kuma kara da cewa za a bi mambobin kungiyar da wadanda aka samu da hannu ciki domin yi masu hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Your browser doesn’t support HTML5

NIJER: Ministan Cikin Gida Ya Gargadi 'Yan Fafutuka Su Shiga Taitayin Su