Shugaban kungiyar da ta shirya gangamin Abbas Abdulaziz, ya nesanta kansa da wannan abu da wasu mahalartan taron gangamin suka aikata. Yace tun da farkon taron ya gargadi mahalarta kada su je ko ina su tsaya inda ake taron saboda baya so a cutar da wani dan Nijer.
Shi kuwa kakakin jami’iyar PNDS mai mulki Asumana Muhammadu ya dora laifin wannan kone-konen tayoyi da zanga-zangar kan shugabannin da suka nemi izinin shirya wannan gangami. Asumana Muhammadu yace gwamnati tayi musu adalci ta basu daman su fito su nuna adawarsu, toh me ya kawo kone konen kayan jama’a alhali kuwa kun fada cewar kuna wannan abu ne saboda jama’ar.
Dambaji Son-Allah, shine shugaban kungiyar kare hakkin jama’a na Kadet ya yi tsokaci a kan muhimmancin batun da ya sa suka shirya zanga-zangar shine zargin gwamnatin tana so ta maida nauyin harajinta duka a kan talakawa, kamar yadda suke gani da gwamnati ta bayyanar a cikin kasafin kudi da ta gabatarwa majalisar dokoki.
Dambaji Son-Allah yace idan gwamnati na son talakawa su biya haraji, tah yakamata ta maido da yaki da masu handamar dukiyar kasa. Ya kara da akwai bukatar gwamnati ta yiwa kamfanonin kasashen Karin haraji kuma ta saukakawa talakawa.
Facebook Forum