Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kundunbalar al-Shabab Sun Sake Aikata Danyen Aiki A Birnin Mogadishu: Rayuka 23 Aka Rasa!


Wasu daga cikin daruruwan 'yan al-Shabab sabbin dauka kenan ke atisaye.
Wasu daga cikin daruruwan 'yan al-Shabab sabbin dauka kenan ke atisaye.

Da an yi tsammanin 'yan ta'addan al-Shabab sun fara daddara, sai gashi sun maida birnin Mogadishu turmin-tsakar-gida-sha-lugude. Ko a jiya sai da su ka kashe wasu bayain Allah akalla 23 a wani kazamin hari na bazata.

Mutane akalla 20, ciki har da wani dan siyasar Somaliya, sun halaka a wasu tagwayen hare-haren bama-bamai da aka kai da motoci, wadanda su ka bararraka Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya jiya Asabar, makonni biyu bayan da wani mummunan harin bam ya kashe mutane sama da 350.

Madobe Nunow, Ministan Cikin Gida na jahar Kudu maso yamma, na cikin mamatan, a cewar jami’ai. Mutane kuma sama 40 ne su ka jijji raunuka a tagwayen fashe-fashen.

Fashewa ta farko ta auku ne a sanannen otal dinnan na Nasa Hablod Two, wanda mayakan al-Shabab su ka abka ciki bayan da su ka tayar da bama-baman da su ka jibga cikin wata mota a mashigar otal din.

Ayan Abdi Ahmed, wanda ke cikin otal din lokacin da aka tayar da bama-baman cikin motar, ya gaya ma Muryar Amurka cewa, “Bayan da aka tarwatsa mashigar otal din da bama-bamai, na ga wasu mutane da bindigogi, saye da kakin sojin kasar na shiga otal din. Sai su ka ruga hawa na biyu inda wasu jami’ai, ciki har da ministoci da ‘yan Majalisar Dokoki ke ciki.” Ahmed ya kara da cewa, “Sai ‘yan bindigar su ka shiga harbin su daya bayan daya. Sai na rabe a wani lungu kafin na sulale daga otal din.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG