WASHINGTON D.C —
A jamhuriyar nijer kotun raba gardama a game da al’amuran hukuma ta yi watsi da wata karar da kungiyoyin malaman makaranta suka shigar domin ta fayyace matsayin jarabawar da hukumomin kasar suke shirin gudanarwa.
An shirya jarabawar ne da nufin tantance malaman makarantar da suka cancanci aikin koyarwa a wani yunkuri na magance koma bayan ilimi a kasar ta nijer.
To sai dai kungiyoyin malaman sun sha alawashin kauracewa wannan jarabawa, lamarin da ya jawo cece-ku-ce da kuma musayar ra’ayoyi daban daban.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni, ya aiko mana da cikakken bayani akan wannan dambarwa.
Your browser doesn’t support HTML5