NIJER: Jami’an Tsaro Sun Kama Wani Mutum Da Yayi Fice Wajen Garkuwa Da Mutane A Nigeria Da Nijar.

Jami'ai sun kwato makamai

A ranar Litinin ne jami’an tsaron kasar Nijar suka kama wani dan bindiga mai suna Mahamane Salisu Isaka da ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane.

Wanda aka kaman, dan asalin jihar Maradi ne dake kudancin Nijar kuma ya kasance babban mai aikata manyan laifufuka ciki har da garkuwa da mutane domin neman biyan kudin fansa.

An dai kama shi ne a wata unguwa da ke cikin birnin Agadas inda ya ke boye.

Adadin 'yan bindigan da jami’an tsaro suka kama a baya bayan nan sun kai 16.

Kasashen Nigeria da Nijar sun dade suna neman wanda aka kama ruwa a jallo saboda ya kasance cikin wani gungun 'yan bindiga da suka shahara wajen yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa inda ya dawo Agadas domin cigaba da aika aika.

Tuni jami’an tsaro suka kaddamar da soma bincike don gano maboyar 'yan bindigan dake garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Musa Abubakar shine shugaban rundunar 'yan sanda ta jihar Agadas, ya kuma bayyana cewa zasu sanya kafar wando guda tsakaninsu da 'yan bindigan domin sai sun yi maganin duk wani dake da nufin shirya tada zaune tsaye a cikin al'umma.

Ba kasafai ake samun damar kama wadanda ake zargi da laifin sace mutane domin neman kudin fansa ba, dake neman ta zama gagara badau a wasu yankuna na kasar Nijar. To sai dai hukumomi a Agadas suna kira ga al’umma da su bada tasu gudunmawa wajen fallasa duk wani mutumin da basu yarda da shi ba. Inji Henri Martin Muktar wanda shine babban alkali mai shigar kara a Agadas.

Kamata ya yi al'umma su bada gudunmuwa ta musamman ga kokarin jami’an tsaro ta hanyar basu labaran sirri ga duk wasu mutanen da ba a yarda da su ba saboda aka kama irin wadannan miyagu don al'umma su gudanar da al’amurransu cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ana su bangaren, masana sha’anin tsaro na ganin samar da wata manufa ta bai daya tare da mikata ga gwamnati na iya zama mafita ga wannan matsalar da a yanzu ta shafi yanayin daukacin zamantakewa.

Saurari rahoton Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

RAHOTON MASU GARKUWA DA MUTANE.mp3