Wannan na zuwa ne biyo bayan bullar cutar shan inna a jahar Maradi da bullar wani kala mai zafi na cutar a makwabciyar Nijer, wato Najeriya.
Sanadiyar kamuwar wani yaro da cutar polio a jahar Maradi, ya sa hukumomin jamhuriyar Nijer tare da masu tallafawa kasar a fannin kiyyon lafiya, shirya gangamin bada magungunan alluran rigakafi na cutar shan inna a jahar ta Maradi da jahohi 2 dake makwabtaka da wannan jahar da suka hada da Tahoua da Zinder.
Malam Assumane Abdulmumuni mai kula da sadarwa a hukumar assibitin Birni N'Konni dake cikin jahar Tahoua, ya ce yaro ne daga Jahar maradi aka samu da alamun cutar, kuma ya kamata daga an ga alumun cutar a murkushe cutar, a bashi magani da gaggawa don dakile cutar.
Suma hukumomin ta bakin shugaban gundumar Birni N'Konni Alhadji Ibrahim Abba Lele sun ce wadanan jahohin sun tsunduma gadan - gadan a cikin wannan aikin domin ganin gangamin da a ka soma tun 11 ga watan Yuli da za a kamalla 14 ga wannan watan ya samu gagarumar nasara.
Ya kara da cewa dole ne a ja hankalin al’umma baki dayansu bisa wannan babbar cutar da ake tsamina an shawo kanta sai ga shi ta sake bullowa cikin wasu jihohi.
Wannan gangamin na zuwa ne a daidai lokacin da wani sabon nau'in cutar shan inna mai zafin gaske ya bayyana a Tarrayar Najeriya dake makwabtaka da wadannan jahohin 3 na jamhuriyar Nijer.
Abinda ya yi sandiyar hukumomin kasar kara azama wajan yiwa yaran da ke garuruwan da ke kan iyaka da masu shigowa Nijer wannan alluran rigakafin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5