Hukumar ta lafiya ta ce rashin cikakken bayani akan rigakafi kusan illar shi daya da cutar da ya kamata rigakafin ya magance. Wata mai magana da yawun hukumar WHO Fadela Chaib, ta fadawa Muryar Amurka cewa rashin samun kyakkyawar fahimta babban kalubale ne ga harkokin lafiya na duniya da ta yiwu ya kawo koma-baya ga ci gaban da aka samu shekaru da dama da suka gabata akan magance cututtukan da za a iya kiyayewa.
Fadela ta ce, kamar missali, lokacin da hukumar WHO ta kaddamar da shirin allurar rigakafin cutar shan’inna a Pakistan ko cutar shawara a Afrika. Za ka ga rashin fahimta sosai akan munin rigakafin. Kuma, mun san cewa rigakafi na aiki. Idan babu rigakafi mutane zasu dinga mutuwa.
Hukumar ta WHO ta yi kiyasin cewa mutane sama da miliyan 3 ke mutuwa duk shekara sakamakon cututtukan da rigakafi zai iya karewa. A gefe daya kuma, hukumar ta yi kiyasin cewa rigakafin cututtukan kyanda, da ciwon hanta, da kwalara da sauransu suna cetor mutane akalla miliyan 2 a duk shekara.
Fadela Chaib ta kuma ce hukumar WHO ta koma ga kamfanonin Facebook, da Instagram, da Pinterest da wasu manyan shafukan yanar gizo don hana yada jita-jita da bayanan da ba na gaske ba dake bullowa daga kafafen game da rigakafi.
Facebook Forum