Yayin da tawagar ministan cikin gida na jamhuriyar Nijer ke kamala rangadi a arewacin jahar Tahoua a yankunan da yan bindiga suka addabi jama'a, wadansu mazauna iyaka da kasar Mali sun koka game da irin yadda 'yan ta'adda ke karbar haraji gare su da ma kudaden fansa.
TAHOUA, NIGER —
A daidai lokacin da Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer, ta kara tsawaita lokutan dokar ta baci a wadansu yankunan jahar Tahoua da ta Tillabery dake fama da 'yan ta'adda da suka zagaye kasar.
Wani batu da al'ummar da ke zaune a arewacin jahar Tahoua da ke fama da matsalar 'yan yakin jihadi suka shaidawa tawagar ministan cikin gida da ta kamalla ziyarar yankunan su shine, irin yadda 'yan bindigar ke tilasta jama'ar wadansu garuruwan biyan diyar dabbobi ko ta kudade bayan sun shaida musu adadin abinda suke son su biya.
Biyo bayan yawaitar kai hare - hare da karbar haraji da 'yan ta'adda ke yiwa jama'a a arewacin jahar Tahoua, shi ne ya kai shugaban kasar ziyartar wadanan yankunan a shekara da ta gabata, tare da yiwa mutanen yankin alkawalin kawo karshen wannan matsalar, inda hukumomin kasar suka daura damara a wannan yankin dake iyaka da kasar Mali.
Yanzu haka dai, malaman addinin Islama na cigaba da fadakar da jama'a da cewa, wannan diyar da 'yan jihadi ke tilastawa jama'a babu inda take alaka da Musulmi ko addinin Musunci.
Ministan ya kaddamar da girka barikin askarawan Garde Republicain a jihar Tahou.
Banda matsalar 'yan bindiga masu ikirarin jihadi, arewacin jahar Tahoua na fama da matsalar tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya, abinda ya sa hakiman wannan yankin bayyanawa 'yan jarida irin gudumuwar da za su kawo gwamnati don warware wannan matsala a wannan yankin.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5