GOGONE dake da nisan kilomita 13 da garinBOSSO na jihar DIFFA dake gabacin kasar Nijar na kunshe ne a wata rubutaciyar sanarwar da gwamnatin kasar ta rarabawa ‘yan jarida a yammacin yau Alhamis . Gwamnatin a wannan sanarwa ta ce ranar Laraba 25 ga watan Nuwamba a daidai lokacinda mazaunan garin na GOGONEke sallar isha’i ne ‘yan Boko Haram suka bude masu wuta ta hanyar anfani da rokoki ba ji ba gani. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18 cikinsu har da babban limamin garin wandadan’ uwansa dake cikin askarawan Boko Haram yayi masa yankan rago.
Sannan maharan sun raunata mutane 11 yayinda wata yarinya ‘yar shekaru 3 da haifuwa tayi batan dabo baya ga gidaje 76 da motoci 2 da mashine da dama hade da tahunoni da suka cinnawa wuta kafin su arce daga kauyen na GOGONE. A wannan sanarwa gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta nuna alhini tare da isar da gaisuwar ta’aziya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su sannan ta bukaci daukacin limamai su yi addu’o-in musamman a daukacin masallatan Jumma’ar fadin kasar don rokarwa mamatan gafarar ubangiji tare da yin addu’o-in ALLAH ya ba dakarun kasar Nijar sa’ar murkushe abokan gaba a yakin da suke kafsawa da kungiyar Boko Haram a illahirin kewayen tafkin Chadi.
Nijar na daga cikin kasashen da ke yakar Boko Haram a karkashin rundunar hadin gwuiwar kasashen CBLT da suka hada da Najeriya da Chadi da Kameroon baya ga Jamhuriyar Benin da ta shiga yakin a matsayin gudunmowa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5