Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kristan Nijar Ba Zata Karbi Diyya Ba daga Gwamnati


Niger celebrates 51st republic anniversary Friday
Niger celebrates 51st republic anniversary Friday

Kungiyar Kristan Nijar tace ba zata karbi diyya daga gwamnati saboda jimami'u da aka kone amma ta kira 'yan siyasa da gwamnati su tabbatar an gudanar da zaben shekara mai zuwa cikin lumana

Kungiyar limaman Krista a jamhuriyar Nijar ( AMEEN) ta bukaci ‘yan siyasar kasar da su kasance masu nuna halin dattaku danganin an gudanar da zabubukan 2016 cikin kwanciyar hankali.

A karshen wani taron tantaunawa akanhalin tafiyar kungiyar ta AMEEN ne limaman Kristan na kasar Nijar suka yi kira ga bangarorin siyasa su guji aikata dabi’un da zasu kawo rikici tsakanin jama’ar kasar ganin yadda harakokin siyasar kasar dinke canza salo a ‘yan kwanakin nan a yayinda ranakun zabe ke kara karatowa. Reverand SAMA’ILA LABO na daga cikin wadanda suka fitarda wannan sanarwa.

Kungiyar AMEEN da sunan mabiya addinin kritan EGLISES EVANGELIQUES ta isar da gaisuwar ta’aziya ga al’ummar Musulmin Nijar sanadiyar asarar rayukan dimbin ‘yan kasar da aka huskanta a Saudiya.

Dangance da kudaden diyya da gwamnatin Nijar ta yi alkawalin ba ma eglisiyoyin da zanga-zangar nuna kyama ga jaridar charlie hebdo ta haddasawa asara a ranakun 15 da 16 da 17 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, kungiyar limaman krista ta AMEEN ta yanke shawarar kin karbar ko sisi a matsayin matakin nisantar da kanta daga jita jitar da ke cewa kungiyar ta yi rubda ciki akan abinda aka bayar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG