Nijar: Yadda Aka Tarwatsa Taron Modem Lumana

Oumarou Noma - Jam'iyar Moden Lumana

Oumarou Noma ya kira wannan taron ne, don ya kara bayani kan rikicin shugabancin da ya kunno kai a tsakaninsa da wasu 'yan Moden Lumana da ke zarginsa da tawaye, ko da yake, a cewarsa ba shi da irin wannan manufa.

A Jamhuriyar Nijar, wasu magoya bayan jam’iyyar Moden Lumana Afirka sun tarwatsa wani taron manema labarai, da shugaban rikon kwaryar jam’iyyar ta adawa Malan Oumarou Noma ya kira a karshen mako.

Oumarou Noma ya kira wannan taron ne don ya kara bayani a kan ci gaban rikicin shugabancin da ya kunno kai a tsakaninsa da wasu 'yan Moden Lumana da ke zarginsa da tawaye, ko da yake, a cewarsa, ba shi da irin wannan manufa.

A lokacin da shugaban rikon jam’iyyar ta Moden Lumana Oumarou Noma ke kokarin sanar da jama’a dalilan da suka sa ya maka mai gidansa Hama Amadou a kotu ne, sai wasu magoya bayan Moden Lumana suka afka cikin ofishin jam’iyyar inda suka tarwatsa taron manema labaran da ya kira.

Tun a jajibirin faruwar wannan al’amari uwar jam’iyar ta Moden lumana a karshen taron da ta gudanar, ta ba da sanarwar korar Oumarou Noma daga sahun ‘ya'yanta, bayan da kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya cancanci ya ja ragamar babbar jam’iyar ta adawa.

A washegarin hukuncin kotun, ‘yan sanda sun tarwatsa wani gagarumin taron da magoya bayan Hama Amadou suka kira a ofishin jam’iyar Moden Lumana ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa, matakin da ya sa Noma Oumarou ya samu dalilin kiran taron manema labarai.

A tabakin shi, ya ce ina jaddada maku cewa na sha fafutuka saboda Hama Amadou, a yanzu haka ina ci gaba da gwagwarmaya domin shi amma fa tare da mutunta doka domin ita dimokraddiya mulki ne da ke bukatar mutunta doka.

Uwar jam’iyar Moden Lumana ta bayyana shirin gudanar da taron "congre" a ranar 4 ga watan Agusta a Yamai, don tabbatar da 'dan takararta na zaben 2021 a hukunce.

Sai dai Oumarou Noma ya kira makamancin wannan taro a garin Dosso a rana daya na Yamai.

Kafin nan shugaban riko da rakiyar jami’an tsaro ya kulle ofishin jam’iyar ta Moden Lumana a cikin daren asabar wayewar jiya lahdi.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Yadda Aka Tarwatsa Taron Modem Lumana