Nijar: Wane Hali Sojojin da Aka Cafke Kan Zargin Yunkurin Juyin Mulki Ke Ciki

Mr.Morou Amadou, ministan ma'aikatar shari'ar Nijar kuma kakakin gwamnati.

Iyalai da dangin sojojin da aka cafke bisa zargin yunkurin yin juyin mulki basu san halin da suke ciki ba yau kusan mako daya da tsaresu saboda ba'a basu izinin ganinsu ba.

Labarin yunkurin juyin mulki da gwamnatin kasar ta bayar ta bar baya da kura domin babbar jam'iyyar adawa tace tsari ne kawai hukumomi suka kitsa a matsayin shashatau domin a manta da wasu mahimman batutuwa na daban.

Dan majalisar dokokin kasa ta jam'ar na jami'ar Abdulkadiri wanda yace a 2011 shugaban kasa ya fito yace an yi masa juyin mulki amma kowa ya san inda zancen ya kare domin a karshe sojojin sakinsu aka yi domin zargin ba gaskiya ba ne.

Yau an wayi gari shugaban kasa ya sake zargin ana yunkurin yi masa juyin mulki. Amma tun farko wajen makonni biyu da suka gabata shugaban kasa ya bada umurni akan wasu sojoji amma sojojin suka ki aikatawa. Yace zata yi wuya a ce zargin da shugaban kasa ya yi akwai gaskiya ciki. Yace yanzu suna jira su ga sakamakon binciken da fatan wadanda suke binciken zasu fito da gaskiya.

Dan majalisar ya cigaba da cewa duk cecekucen da ake yi da zargin juyin mulki duk dabaru ne na kokarin karkata hankulan jama'a daga wasu batutuwa daban da su ke ciwa 'yan Nijar tuwo a kwarya musamman zancen zabe.

A nasu bangaren jam'iyyu masu goyon bayan shugaban kasa Issoufou Mahamadou sun bukaci mahukunta su hukunta duk wadanda su ke da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin. Salisu Muhammad Sabi mai magana da yawun kawancen jam'iyyu masu rinjaye yace a kara yadda da yiwa aiki mai kyau katsalandan. Yace koyaushe wata gwamnati ta tashi tana aiki mai kyau sai sojoji su shigo. Yace miyagun mutane ne suke tashi koyaushe suna hambarar da gwamnati.

Majiya daga gwamnatin kasar tace nan ba da dadewa ba za'a gurfanar da sojojin da ake tuhuma gaban kotun shari'a ta sojoji. A wani halin kuma wani alkali ya salami Muhammadu Dudu na jam'iyyar CDS Rahama wanda aka damke saboda ya yi musu akan labarin juyin mulkin a wata fira da yayi da wata kafar yada labaru. To sadai an tasa keyar takwaransa Ibrahim Hamidu na jam'yyar MNSD Nasara akan zargin zuwa kurkukun Yamai.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Shin Wane Hali Sojojin da Aka Cafke Kan Zargin Yunkurin Juyin Mulki Ke Ciki - 2' 35"