Mai magana da yawun gwamnatin Nijar yace sun kama mutanen ne domin su hanasu aikata barnar da suka shirya yi.
Wadanda gwamnatin kasar tace ta kama sun hada da Janar Salu Suleiman, Kanar Idi Dan Hawal, Lutenat Kanar Dahiru Zarmai da Nari Mai Duka, Issoufou Umar, Ahmadu Shekarau, Isa Ahmadu Kounche, da Koro da Awal Hambat. Dukansu sojoji ne. Babu farin hula ko daya cikinsu. Kodayake babu sunan dan siyasa cikinsu amma ana cigaba da bincike.
To saidai alamarin yana faruwa ne a daidai lokacin da 'yan siyasar kasar ke ja-in-inja tsakaninsu saboda zaben shekara mai zuwa. Wani abu ma da ya jawo takaddama a bangaren 'yan adawa da gwamnati shi ne rajistan sunayen masu kada kuri'a. Su 'yan adawa sun ki amincewa da sunayen da aka jiwa rajista. Sun ma gujewa kwamitin binciken rajistan sunayen.
Muhammad Dudu kakakin kawancen 'yan adawa ya zargi gwamnati da tsoron shugabanin jam'iyyun 'yan adawa.
A tasu sanarwar da suka fitar jam'iyyun dake mulki sun ce 'yan adawa sun dauki matakin ne domin basu da bayanan da zasu ba talakawan kasar. 'Yan adawa sun yi shekara biyar basu fita daga birnin Yamai ba suna jiran gwamnati ta fadi.
Ganin yadda lamura ke tafiya sakataren watsa labarai na kawancen MRN Ali Isbego ya kira 'yan adawa da su yayyafawa zuciyarsu ruwan sanyi.Yace Allah ke bada iko. Idan Allah ya basu sai su yi. Yau Allah ya ba Mahamdou Issoufou sai su hakura su hada hannu da gwamnati a gyara kasar.
Amma a wani bangaren hukumomin kasar sun kama wasu 'yan siyasa biyu da suka hada da Dudu Muhammad da Ibrahim Hamidu wadanda aka tsare tun yammacin Asabar.
Ga karin bayani.