Nijar Ta Yi Watsi Da Tayin Girke Sojojin Rundunar Takuba

SOJOJI A MALI

Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta yi watsi da tayin mayar da sansanin sojan rundunar hadin guiwar kasashen turai wato Takuba daga Mali zuwa kasar ta

Sai dai wasu masu bin diddigin al’amuran tsaro na ganin wannan tayi tamkar wata hanyar da za ta bai wa hukumomin Nijar damar morar abubuwa da dama a karkashin wannan yunkuri.

Yanayin tsamin dangakar da ake ciki a tsakanin hukumomin Mali da na Faransa wanda kuma ya fara shafar huldar kasar ta Mali da nahiyar turai ya sa wadanan kasashe soma yunkurin kwashe dakarun rundunar hadin guiwar nahiyar Turai wato Takuba daga kasar ta Mali da nufin mayarda su jamhuriyar Nijer, a yayinda rahotanni ke cewa sojojin Russia sun fara wargaza malabar ‘yan ta’addan arewacin Mali.

Koda yake kawo yanzu ba a bayar da wata sanarwa ba a hukumance akan wannan yunkuri cibiyar kula da yada labarai a fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa, Nijar ta yi watsi da wannan tayi.

Matakin girke sojojin kasashen waje a yankin Sahel wani abu ne da kungiyoyin fafitika suka jima suna gwagwarmayar a kansa saboda a cewarsu alama ce ta sabon salon mulkin mallaka. Moudi Moussa jigo ne a kungiyar TLP.

To amma mai sharhi akan sha’anin tsaro Moussa Aksar na cibiyar nazari da bincike Centre Norbert Zongo na ganin tayin na Faransa da kawayenta a matsayin wata hanyar da za ta bai wa Nijar damar cin gajiyar huldar dake tsakaninta har ma da gindaya masu tsauraran sharuda a fannin tsaro.

Wasu majiyoyi na daban na cewa Kasar Faransa dake jan akala a sabuwar tafiyar da aka sa gaba na neman shayo kan hukumomin Nijar su amince da tayin na girke rundunar Takuba da ake hasashen kwatsewa wuri 1 da rundunar sojan Barkhane wanda ake dauka a matsayin mafarin rangadin da ministar tsaron Faransa Florence Parly ta yi a makon jiya a nan Nijar inda suka gana da shugaban kasa Mohamed Bazoum ba tare da baiwa ‘yan jarida damar sanin abubuwan da suka tantauna akan su ba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Yi Watsi Da Tayin Girke Sojojin Rundunar Takuba :3:00pm