Nijar Ta Yi Karin Bayani Game Da Harin Inates

Taron Da Nijar Tayi Karin Bayani Game Da Harin Inates

Mako daya bayan harin da ya haddasa mutuwar sojoji 71 a barikin Inates, gamayyar jam’iyun da ke mulkin jamhuriyar Nijar ta yi karin haske dangane da abubuwan da suka faru lokacin wannan mummunan tashin hankali.

Saboda haka suka gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta da su yi taka tsantsan don kauce wa fadawa tarkon masu tada kayar baya.

Taron Da Nijar Tayi Karin Bayani Game Da Harin Inates

Wasu bayanan da aka yada a shafukan sada zumunta a washegarin wannan kazamin hari, na cewa wani jirgin leken asiri ya yi shawagi a sararin samaniyar barikin sojan Inates sa’o'i kalilan kafin maharan su kai farmaki.

Ministan cikin gida Bazoum Mohammed, a sanarwar hadin gwiwa da jam’iyu masu mulkin Nijar, ya karyata labarin.

Haka kuma wadannan bayanai na cewa,‘yan ta’addan sun yi nasarar kona rumbun harsasai, da tankokin mai a barikin sojan na Inates, matakin da ake ganin shi ne dalilin da ya sa suka samu yin galaba.

Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed

Bazoum Mohammed ya musanta haka, amma ya tabbatar da cewa harin ya haifar da lalacewar hanyoyin sadarwa.

Mutane da dama a kasashen Sahel na zargin kasashen Yammacin Duniya masu sansanin soja a wannan yanki da fakewa bayan yaki da ta’addanci, sai dai ministan ma’adinai, Moussa Baraje, a wata sanarwa, ya ce babu gaskiya a wannan zargi.

Taron Da Nijar Tayi Karin Bayani Game Da Harin Inates

Harin Inates, shi ne mafi muni da aka taba fuskanta a jamhuriyar Nijar, shekaru 4 bayan da ‘yan ta’dda suka fara kai farmaki a wannan kasa.

Yayin da hukumomi ke cewa sojoji 71 ne suka hallaka, wasu kuwa na cewa yawan wadanda suka rasu ya haura 100.

Saurari rahoto cikin suati.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Yi Karin Bayani Game Da Harin Inates