Nijar Ta Tsaurara Matakan Shiga Kasarta

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani

A cewar masu sharhi, wannan doka ba ta shafi 'yan kasashen da suka fito daga yankin kasashen ECOWAS ba.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ya kafa dokar haramta wa 'yan kasashen waje shiga kasar ba tare da takardun bulaguro ko na izinin zama ba

Matakin wanda aka ayyana a matsayi na tsaurara matakan tsaro ya tanadi hukuncin kora ko dauri ko kuma biyan tara ga duk wanda aka kama da bijirewa wannan doka wacce a wani bangare ta umurci 'yan kasar su sanar da ‘yan sanda kafin bai wa baki 'yan kasashen waje masauki.

Cikin wata takarda da Sakatariyar Gwamnatin Nijar ta fitar a yammacin Litinin 13 ga watan Janairu aka sanar cewa Janar Abdourahamne Tiani ya kafa dokar hana wa baki ‘yan kasashen waje shiga kasar ko su zauna ba tare da mallakar takardun bulaguro ba.

Dr. Bachir Amadou Adamou wani lauya mai ba da lacca a jami’ar UFR da ke birnin Nantes na Faransa ya ce duk wanda ba dan wata kasar CEDEAO ba ne da mutanen da kasashensu ba su da huldar shige da fice da Nijar, su ne ake nufi baki ‘yan kasashen waje.

Abin nufi rukunin wadanan mutane ne ya zama wajibi idan za su shiga Nijar sai sun tanadi takardu wato biza ko kuma takardar izinin zama Titrede sejour. Dokar dama akwaita amma ba a zartar da ita ne yadda ya dace.

Dokar ta kara fayyace abin da ficewar Nijar daga CEDEAO ke nufi. Don sanin cewa ficewar na ba da wani tasiri kan ‘yancin kai-da-kawon jama’ar kasashen CEDEAO da dukiyoyinsu tun da a baya kasashen AES a wata sanawar hadin gwiwa sun tabbatar da cewa ficewarsu daga ECOWAS ba za ta shafi kai-da-kawon mutanen CEDEAO ba, ma’ana babu bukatar biza wajen shiga ko zama.

Bijirewa wannan doka abu ne da ka iya janyo wa mutun kora daga Nijar ko kuma a mayar da shi kasarsa ta asali, ko kai shi kan iyaka a ajiye.

Haka kuma dokar ta tanadi hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 5 da biyan tarar million 5 na cfa zuwa million 50.

Kamar yadda irin wannan hukunci ka iya hawa kan wani mutun ko kungiyar da ta taimaka wa bako ‘dan kasar waje shiga Nijar ba da takardu.

Barazanar kutse a yunkurin tada hargistin da gwamnatin kasar ke zargin wasu kasashen waje da hannu ne mafarin bullo da wannan doka, kuma matakin da shugaban kungiyar SYNERGIE de la Societe civile, Elkabir Mohamed ya yaba da shi.

Sai dai mawallafin jaridar Niyya Info Tahirou Garka na da wani ra’ayin na daban.

Sanar da hukumar ‘yan sanda samun bakunci daga wani ‘dan kasar waje tilas ne ga kowane dan Nijar a karkashin wannan doka ko kuma mutun ya fuskanci fushin hukuma.

Ko baya ga batun tsaro dokar ta 13 ga watan Janairun 2025 abu ne da ke hangen saka tsari kan sha’anin cirani da shigowar bakin haure inji masana.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Tsaurara Matakan Shiga Kasarta. MP3