A hirarsu ta baya da wata mujallar kasar Faransa, shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ta bukaci Najeriya, da Jamhuriyar Benin, da su dawo da jagoran ‘yan adawa Hama Amadou zuwa gida, inda wata kotu ta yanke masa hukunci daurin shekara 1 a kurkuku sakamakon samunsa da hannu a wata badakalar safarar jarirai.
Wannan shi ne matakin da magoya bayansa irin su Mahamadou Maidouka ke kallonsa a matsayin wani yunkurin sharewa jam’iyyar PNDS mai mulki hanyar lashe zaben 2021.
Sai dai shuwagabanin PNDS Tarayya sun nisanta kansu da halin da dan takarar na Moden Lumana ke ciki.
Shekaru sama da 4 kenan Hama Amadou ke gudun hijira tsakanin kasashen Faransa, da Ghana, da Najeriya, da Jamhuriyar Benin, bayan da ya gudu daga Nijar a wani lokacin da ake gab da gurfanar da shi a gaban kotu.
Sai dai har yanzu magoya bayansa na cewa farin jininsa na ci gaba da karuwa a wajensu, wanda kuma suke ganin shi ne mafarin bita-da-kullin da yake fuskanta daga masu mulki a cewar su.
Badakalar safarar jarirai wani al’amari ne da aka shafe shekaru ana fafatawa akansa a kotuna, tun daga Nijar har zuwa kasashen waje.
Yayin da hukumomi ke ganin bakin alkalami ya bushe, saboda yadda galibin wadanda ake zargi suka ba da kai ga hukuncin da ya hau kansu.
Shi kuwa Hama Amadou da makusantansa na cewa kokuwa ba ta kare ba.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5