Nijar Ta Fara Kwaso ‘Yan kasarta Da Ke Bara A Ghana

Masu bara da hukumomin Nijar suka kwaso daga kasar Ghana

Mutane sama da 500 wadanda suka hada da mata da yara  har da tsofaffi ne jirgin Max Air ya sauke a filin jirigin saman Diori Hamani da misalin karfe 3 na ranar  wannan Laraba 8 ga watan Yuni,

Ayarin farko na ‘yan Nijer dake bara a kasar Ghana ya sauka birnin yamai a yammacin yau laraba inda hukumomin kasar suka tarbe su kafin daga bisani a fara kwashe su don mayar da su garuruwan da suka fito.

Mutane sama da 500 wadanda suka hada da mata da yara har da tsofaffi ne jirgin Max Air ya sauke a filin jirigin saman Diori Hamani da misalin karfe 3 na ranar wannan Laraba 8 ga watan Yuni,

Wadanan mutane da aka bayyana a matasyin ‘yan asalin jihar Maradi da jihar Zinder sun tare ne a Ghana inda suka mamaye titunan biranen kasar da sunan bara lamarin da gwamnatin Nijer tace ba za ta laminta da shi ba mafari kenan aka maido su gida. Ga jawabin da ministan aiyukan jin kai Alhaji Lawan Magaji ya yi masu lokacin da suka iso.

Wadanda muka zanta da su daga cikin wadanan mabarata sun yi nadamar shiga wannan haraka ta kaskanci koda yake a cewarsu talauci da rashin madogara ne mafarin ficewarsu daga gid aba shiri.

Lokacin da masu bara 'yan Nijar suka sauka a Yamai bayan da aka kwaso su daga Ghana

Ministan aiyukan agaji ya bayyana cewa gwamnatin Nijer ta lashi takobin tsaurara matakai don kawo karshen wannan al’amari na yiwa kasa mummmunar talla a idon duniya.

Shugaban kungiyar agaji ta DHD Afriqiue Kabirou Issa dake daya cikin wadanda suka tarbi wadanan mutane ya shawarci hukumomi akan bukatar maida hankali wajen ayyukan fadakarwa.

Bayan da aka ba su damar cin abinci da samun dan takaitacen lokacin hutu motocin bus bus sun kwashe wadanan mutane da nufin mayar da su garuruwansu na asali yayinda jirgi ya jya zuwa kasar Ghana domin kwaso ragowar wasu daruruwan mabarata a ci gaba da zartar da shirin da gwamantin Nijer ta kaddamar don kwashe illahirin ‘yan kasar dake zaune a kasashen waje da sunan bara.

A watan maris din da ya gabata ma Nijer ta kwashe wasu ‘yan kasar sama da 1000 daga Senegal inda suka tare a matsayin mabarata.