Wannan na zuwa ne bayan da aka shafewunin jiya cikin halin rudani wasu sojojin da suka bayyana a kafar talabijin mallakar gwamnatin kasar sun bada sanarwar kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum sakamakon mawuyacin halin da suka ce an shiga a kasar.
Kawo yanzu kwamitin sojojin da ya karbe madahun iko bai bayyana sunan mutanen da ke jagorancinsa ba.
Sojojin wadanda suka kira kansu mambobin kwamitin tsirar da kasa wato "Conseil National Pour La Suavegarde De La Patirie, CNSP" , sun ce sun kifar da gwamnatin Nijar a jiya laraba 26 ga watan Yuli sakamakon lura da abinda suka kira tabarbarewar sha’anin tsaro da mawuyacin halin rayuwar da na matsin tattalin arzikin da ake ciki a kasar.
Suna masu bada tabbacin mutunta dukan yarjejiyoyin kasa da kasa da Nijar ta saka wa hannu. "Haka kuma za su kare mutunci da lafiyar hukumomin da suka hambarar daidai da ka’idodin ‘yancin dan adam."
Sanarwar sojojin na CNSP wace Colonel Amadou Abdourahamane ya karanta ta kara da cewa sun rusa dukkan hukumomin da ke da alaka da jamhuriya ta 7 , sun kuma umurci sakatarorin ofisoshin ministoci su ci gaba da gudanar da lamura yayinda suka bukaci abokan hulda na kasa da kasa da kadda su yi shishigi a harkokin cikin gidan Nijar.
Iyakokin kasar zasu kasance rufe daga jiya laraba sai yadda hali ya yi sannan an kafa dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa 5 na safe inji su.
Da sanyin safiyar jiya laraba 26 ga watan yulin 2023 ne wasu dogarawan fadar shugaban kasa a karkashin jagorancin Janar Omar Tchani suka yi garkuwa da shugaba Mohamed Bazoum a gidansa sannan suka hana ma’aikatan fadar shiga ofisoshinsu, haka kuma aka tsaurara matakan tsaro a kewayen fadar Shugaban kasa da na talabijin mallakar gwammanti, lamarin da ya sa zargin yunkurin juyin mulki ya fara karfafa a wajen jama’a .
Kafin bayyanar sanarwar sojojin na CNSP jama’a sun yi zanga zangar goyon bayan shugaba Mohamed Bazoum a biranen Yamai da Zinder da Tahoua a daidai lokacin da shugabanin jam’iyun kawancen MRN masu rinjaye suka fitar da sanarwa domin kalubalantar yunkurin kifar da zababben shugaban kasa.
Wata tawagar jami’an hukumomin Najeriya a karkashin inuwar kungiyar ECOWAS ta iso birnin Yamai a yammacin jiya wadanda suka yi mahada da shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon da ake sa ran zai shigo a wannan Alhamis domin duba hanyoyin sulhu.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5