Nijar: Nakasassu Sun Koka Game Da Matsalolin Da Suke Fuskanta

Tseren Keke Na Nakasassu A Nijar

A yayin da kasashen Duniya ke bukukuwan karrama ranar nakasassu ta duniya a yau 3 ga watan Disamba, kungiyoyin nakasassu a Jamhuriyar Nijar sun koka game da matsalolin da su ke fuskanta, kamar na ‘yancin shiga wurare da dama a kasar sakamakon rashin mutunta ka’idodin gine ginen zamani.

Tseren Keke Na Nakasassu A Jamhuriyar Nijar

Tun a shekarar 2008 ne Jamhuriyar Nijar ta saka hannu akan yarjejeniyar mutunta ‘yancin nakasassu a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, sai dai shekaru sama da goma bayan wannan alwashi har yanzu ana jan kafa wajen zartas da wasu mahimman sassan wannan kundi.

Ratsa tituna a manyan biranen Jamhuriyar Nijar wani abu ne da a yau ke dauke da matukar hadari ga rayuwar nakasassu.

Tseren Keke Na Nakasassu A Jamhuriyar Nijar

A yanzu haka shirye shiryen zabubukan 2020 da 2021 sun kankama a Nijar sabili kenan shugaban kungiyar nakasassu masu wasannin motsa jiki Harouna Ousman ke jan hankula akan maganar daukar matakan da za su bai wa masu bukata ta musamman damar kada kuri’a cikin kyakkyawan yanayi.

Domin karrama ranar ta 3 ga watan Disamba kungiyoyin nakasassu sun gudanar da gudun tseren keke na maza, da na mata a filin kwallon kafa na Stade Seini Kountche da ke birnin Yamai, kafin wasan kwallon volley ball a cibiyar wasannin motsa jiki ta Academy des Arts martiaux.

A saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Nakasassu Sun Koka Game Da Matsalolin Da Suke Fuskanta