Nijar Na Yunkurin Magance Matsalolin 'Yan Kasarta Da Ke Zaune A Ghana

PATICIPANTS

Gabanin nan, mataimakin Ministan ya bayyana yanayin da Nijar take ciki a yau, inda ya ce, a shirye kasar take ta amshi masu zuba hannun jari.

YAOUNDÉ, CAMEROON - Mataimakin ministan harkokin kasashen waje Issoufou Almoctar ya jagoranci wata tawagar gwamnatin zuwa kasar Ghana, da zimmar jin irin koken 'yan Nijar mazauna Ghana.

Ministan ya kara da cewa, shugaban kasa Mohammed Bazoum da Firaim Minista Ouhoumoudou Mahamadou ne suka turo shi domin su san matsalolinsu kuma a yi kokarin magance su.

Ya kuma yi kira gare su da su je su zuba hannun jari a Nijar; da yadda za a taimakawa ‘yan asalin Nijar da suka bazu duniya su shiga manyan kungiyoyi da ma’aikatu na duniya.

Gabanin nan, mataimakin Ministan ya bayyana yanayin da Nijar take ciki a yau, inda ya ce, a shirye kasar take ta amshi masu zuba hannun jari.

NIGER MININTER

Jakadar Nijar a Ghana, Hajiya lamido Salamatu Bala Goga, ta sanarwa Muryar Amurka cewa, gwamnati ta dauki matakan dakile matsalar barace-barace da ‘yan kasar ke yi a kasashe makwabta, musamman nan Ghana.

Ta ce, an dauki mataki kuma za a hukunta duk wanda aka kama; musamman wadanda suke kwangilar jigilarsu.

AMBASSADOR NIGER

Wadanda suka halarci taron tattaunawar sun tofa albarkacin bakinsu ga Muryar Amurka, kuma sun nuna goyon bayansu da wannan mataki da gwamnatin Nijar ta dauka, sannan za su ba da ta su gudunmawar ga hakan.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullahi Bako

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Gudanar da Muhawara Da ‘Yan Asalin Kasar Dake Zaune A Ghana