Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa kusan kashi 80 cikin 100 na al’umar Jamhuriyar Nijar, ba su da masaniya kan abinda ya kundin tsarin mulkin kasar ya kunsa.
Hakan ya sa hukumomin kasar suka hada kuduri aniyar fassara muhimman dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.
A cewar Darektar ma’aikatar fassara ta CCL a Nijar, Hajiya Fatima Sahabi, “a cikin tsarin mulkin dimokradiyya muke, ya kamata a ce kowane ya san menene kundin nan ya kunsa.”
“Za mu fassara su a harshen Hausa da Zabarbanci da da Kanuri a bugu na farko abinda muke nufi a nan shine karfafawa da sanin demokradiyya da doka, wadannan abubuwa idan an san su za su kawo ci gaba.” In ji Dr. Maina Bukar Karte na kungiyar ANC mai dauke da masana doka.
Ministan harkokin wajen Nijar Ibrahim Yakuba ya nuna farin cikinsa kan tabbatuwar wannan aiki zai kara tabbatar da daidaituwar tafiyar mulkin demokradiyya a kasar.
“Yana da muhimmanci a ce cikin demokradiyya a ce mun cimma wannan nasar wadanda suke jin harshen da ba turanci ba a ce sun san mai kundin nan ya kunsa sun kuma san mai dokoki suka kuna.”
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai domin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5