Ambaliyar ruwa tayi mummunar barna a yankin Tahoa a jamhuriyar Nijar.
Ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwariya, ya haddasa koguna da koramu da suke yankin suka cika suka batse. Lamari da ya haddasa mutuwar dubban dabbobi da rushewar gidaje.
Gwamnan jahar Tahoa, Musa Abdulrahman, wanda ya bayyana haka a lokcinda ya kai ziyarar ganema kansa irin barnar da ta auku da kuma jajantawa jama’a da lamarin ya rutsa da su.
Hukumomi a yankin sun shawarci jama’a da su tafasa ruwa sosai kamin su sha, domin gudun kamuwa da cuta saboda gurbacewar ruwa a yankin. Haka nan kuma sun shawarwaci jama’a su binne dabbobin da suka mutu domin gudun yaduwar cututtuka.
Gwamna Abdulrahman, yayi kira ga masu hanu da shuni su tallafawa wadanda wannan bala’I ya shafa.
Haka nan Gwamnan ya ziyarci wasu sassan jihr inda ruwan sama da aka yi ranar 9 ga watan nan har mutane uku suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata.
Wakilin Sashen Hausa Haruna Mammane Bako,ne ya aiko da wannan rahoto.
Facebook Forum