Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana shirin daukan sabbin sojoji kimanin 5000 a ci gaba da karfafa matakan da zasu taimaka a murkushe matsalolin tsaron da suka addabi kasar sanadiyar lalacewar al’amura a yankin sahel da kewayen tafkin Chadi.
A sanarwar da aka bayar ta shafin info militaire mai kula da labaran da suka shafin sha’anin tsaro ne hukumomin Nijer suka bayyana niyyar gudanar da aikin tantance matasan dake bukatar shiga aikin soja a fadin kasar.
Sabbin matasa a kalla 5000 ne ake bukatar shigarwa a wannan fanni a yayin aikin tantancewar da za gudanar daga ranar 1 zuwa 31 ga watan mayun 2022 adadin da ya zarta soja 2000 da aka saba dauka a shekarun baya.
A cewar tsohon ministan tsaron kasa Kalla Moutari la’akari da yanayin da ake ciki a yau ya kai matsayin da za a kara jan damara.
Matasa ‘yan Nijer masu shekaru 18 zuwa 25 da haifuwa ne ake fatan ganin sun shiga wannan aiki, dalili kenan wani jagoran matasa Mohamed Sidi ke kiran takwarorinsa su bada hadin kai ga wannan yunkurin na kare martabar kasa.
Mai sharhi akan sha’anin tsaro Alkassoum Abdourahaman na gargadin wadanda aka dora wa alhakin gudanar da wannan aiki su dage akan mutunta ka’idodi domin tabbatar an dauki yaran da suka cancanci shiga aikin soja.
Kara yawan dakarun tsaro da bayarda cikakken horo da samar da nagartattun kayan aiki abubuwa ne da shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya sha alwashin maida hankula akansu a yayin da yake gabatar da tsarin jadawalin aiyukan inganta sha’anin tsaron kasa wato Poltique Nationale de la Defense da ya gabatar a watan oktoban 2021 a makarantar horon manyan hafsoshin soja Ecole Militaire Superieure Du Niger dake birnin Yamai.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5